ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press(IP) ya nakalto Salihi yana fadar haka a majalisar dokokin kasar Iran dake nan birni Tehrana jiya Asabar. Ya kuma kara da cewa gina cibiyar bada wutan lantarki ta makamashin nukliya yana da tsada, amma kuma ya fi arha don zai bada wutan lantarki na shekaru kimani 60-70 sannan cibiyar tana bukatar makamashin nukliya na dalar Amurka miliyon 30-40 a duk magawat 1000 MT da zata samar.
Sai dai samar da ita yana iya lamuncewa al-ummar makasar mai zuwa da wutan lantarki tabbatacce.
Don haka ne jagoran ya bukaci a samar da wutan tare da amfani da makamashin nukliya har zuwa megawatts 20,000.
A cikin watan mai zuwa ne ake saran za’a fara gina harsashen cibiyar bada wutan lartarki na Bushar 02 kusa da na farkon.
342/